Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) - ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Ofishin Hulda da Jama'a na Dakarun Juyin Musulunci na Iran ya sanar da cewa: Yayin da ya zamo waɗannan laifuka suna ci gaba, aikinmu zai zama ramuwa ga masu laifin ta’addanci, yawancin hafsoshi da sojojin mamaya na Amurka, saboda tsoron wutar mayaƙan Musulunci, sun bar sansanoninsu, kuma sun mayar da wasu gine-gine a cikin garuruwa wurin aiwatar da laifukansu. Muna gargadin dukkan al'ummar kasashen da ke da wuraren ajiye sojojin Amurka, da su nisanta da gaggawa har zuwa tazarar mita 500 daga wuraren zama na boye da na sojojin Amurka, domin su tsira.
………..
Ra'ayinka